Amurka ta daina ba wa Pakistan tallafin tsaro

Shugaba Donald Trump Hakkin mallakar hoto Others
Image caption A farkon makon nan Shugaba Trump ya zargi Pakistan da yin karya da yaudarar Amurka tana karbar taimakon biliyoyin dala

Amurka ta ce za ta daina ba wa Pakistan taimakon da ta saba ba ta saboda kasar ba ta yin wani abin a-zo-a-gani wajen yaki da mayaka masu ikirarin jihadi, da ke tayar da kayar baya.

Ma'aikatar harkokin waje ta Amurkar ce ta bayar da sanarwar, 'yan kwanaki bayan da Shugaba Trump a wani sako na Tweeter na sabuwar shekara ya caccaki hukumomin Pakistan din.

Shugaban inda ya zargi kasar da yin karya da yaudara ta samu taimakon Amurka, yayin da kuma a bangare daya take bayar da mafaka ga 'yan ta'adda.

Amurka da sauran kawayenta daman suna korafin cewa Pakistan na bayar da mafaka ga mayakan kungiyar Taliban ta Afghanistan da kuma abokansu na kungiyar Haqqani, inda suke zargin Pakistan din na kyale mayakan suna ketara iyaka su kai hari a Afghanistan, zargin da Pakistan din ta sha musantawa, amma kuma Shugaba Trump ya ci gaba da suka da zargin tun lokacin da ya hau mulki.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce, Washington ta yanke shawarar dakatar da ba wa Pakistan taimakon tsaron har sai ta ga Islamabad tana daukar mataki na ba-sani-ba-sabo a kan mayakan masu ikirarin jihadi.

Ko da yake mai sanarwar ba ta ambaci nawa ne taimakon da Amurkar ta dakatar da ba wa Pakistan ba, amma dai ta ce kudin da ta tsayar din bayan dala miliyan 255 ne na taimakon soji wanda daman tuni ta dakatar, a matsayin wani mataki na sauya salon dangantakarta da kasashen yankin, wadda ta fifita alaka da India da Afghanistan.

Haka kuma mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurkar a yayin sanarwar, ba ta iya bayar da wani cikakken dalili na kara dakatar da tallafin ba a yanzu, ko da yake daman sanarwar ta biyo bayan sakon Tweeter da Shugaba Trump ya yi na barazanar yin hakan.

Daman da dari-dari Pakistan ta bi sahun Amurka na yaki da ta'addanci bayan harin 11 ga watan Satumba, wanda a dalilin hakan ta samu tallafin biliyoyin dala daga Amurkar.

Tsawon wani lokaci Amurka tana ta rage tallafin saboda rashin gamsuwa da irin rawar da Pakistan ke takawa a yaki da masu tayar da kayar bayan, amma duk da haka kawancen ya ci gaba, domin Amurkar na bukatar hadin kai daga Pakistan a yakin.

Hukumomin Pakistan suna kukan cewa sun yi matukar asara a yakin da suka dade suna yi da kungiyoyin masu ikirarin jihadi, kuma ransu ya baci sosai ganin cewa Shugaba Trump ya kasa ganin irin muhimmiyar rawar da suke takawa.