'Rashin kwararrun likitoci barazana ce'

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Likitocin Nigeria sun kashe 'yar uwata'

Latsa alamar lasifika domin kallon hira da Malam Alfullati

Wani mutum dan Najeriya ya yi zargin cewa likitocin kasar sun kashe 'yar uwarsa a lokacin da suke yi mata tiyata.

Malam Ibrahim Alfullati, wani mazaunin Abuja, babban birnin kasar, ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ake kokarin cire mata wani kari da ke cikinta.

A cewarsa, "Bayan an yi mata gwaje-gwajen gano cuta, sai aka lura cewa wani tsiro ne sai aka bukaci mu biya kudin da za a yi mata aiki. Da aka yi aiki na farko bai yi nasara ba, sai aka ce sai an sake yi.

"A aiki na biyu din ba a yi mata allurar kashe zafi ba; tana ji tana gani ana huda cikinta. 'Yarta ta cikinta tana can waje amma tana jin kukanta tana cewa 'wayyo Allah za su kashe ni!'Wannan 'yar tata tana ji likitocin suna dariya", in ji Malam Alfullati.

Malam Ibrahim dai daya ne tak daga cikin dimbin mutane da su ko 'yan uwansu suka shiga tasku a tsarin kiown lafiya, ba a Nijeriya kadai ba, a kasashe da dama na Nahiyar Afirka.

Lamarin na faru ne ne a daidai lokacin da wani sabon bincike da aka yi a kasashen Afirka ya nuna cewa mutane da akan yi wa tiyata kan fuskanci hadarin mutuwa fiye da na sauran kasashen duniya, inda adadin mace-mace a nahiyar ya ninka na sauran yankunan duniya fiye da sau biyu.

Wannan na faruwa ne duk da cewa wadanda akan yi wa tiyata a nahiyar shekarunsu na haihuwa ba su kai na sauran yankunan duniya ba, kuma galibi ayyukan da akan yi masu na kananan cututtuka ne a cewar binciken da kwararu suka wallafa a Mujallar Kiwon Lafiya ta The Lancet.

Labarai masu alaka