Kalli hotunan abubuwan da suka faru cikin Afirka a makon nan

Hotuna mafi kyawu da aka zabo na abubuwan da suka faru a fadin Afirka ko kuma dangane da nahiyar a wannan mako:

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan kallo sun saki baki cikin mamaki a lokacin bukukuwan shiga Sabuwar Shekara a kwarin Victoria cikin kasar Zimbabwe…
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasannin kalankuwa a kwarin Victoria sun zo karshe bayan shagulgulan kwana uku a garin na yawon shakatawa…
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sowa ta barke a Nairobi babban birnin Kenya, bayan cincirindon mutane sun kirga cikar dakikokin shiga Sabuwar Shekara a wani biki da aka yi a Cibiyar Taron Kasashen Duniya ta Kenyatta...
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A Afirka Ta Kudu, an fito da wayoyin salula don daukar wasan tartsatsin wuta na shiga Sabuwar Shekara a Dandalin Mary Fitzgerald cikin birnin Johannesburg…
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Tun farko ranar Lahadi a birnin Cape Town na Afirka Ta Kudu, makadan badujala sun yi wasa don bankwana da tsohuwar shekara yayin faduwar rana a gabar tekun Scarborough...
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Washe gari kuma, 'Yan Afirka Ta Kudu sun kwarara zuwa gabar tekun Durban don yin wanka da kuma yin maraba da 2018…
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lokacin bikin tsarki ne na addini ga mabiya Cocin Nazareth Baptist a Afirka Ta Kudu, wanda kuma ake kira da Shembe, yayin bikinsu ranar Lahadi gabanin wata ziyara zuwa tsaunin Nhlongakazi a arewa da Durban.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Talata, mutane sun ci ado suna rera wakoki a wani bikin raye-raye, wanda ya samo asali daga zamanin bauta a yankin Cape inda ake ba wa bayi hutu washe garin ranar Sabuwar Shekara.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yara suna lilo a bikin Sabuwar Shekara cikin wani dandali da ke Abuja babban birnin Najeriya ranar Litinin.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Laraba, ma'aikatan jirgin kasa da ke jigila daga Addis Ababa zuwa kasar Djibouti sun jeru bayan isar jirgin fasinja na farko daga babban birnin kasar Habasha zuwa tashar Nagad ta kasar Djibouti.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A dai wannan rana, 'yan gudun hijirar Eritrea na zukar tabar shisha a wata rumfar shaye-shaye ta wucin gadi da ke wajen cibiyar tsare mutane ta Holot kusa da Nitzana cikin saharar Negev a kan iyakar Isra'ila da Masar.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Lahadi, Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya isa don gabatar da jawabin kasa a fadarsa da ke babban birnin Khartoum yayin bikin cika shekara 62 da samun 'yancin kai.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Abu ne mai kyau ganin allon Liberia da ke "Tattaunawa Batutuwan Yau da Kullum" ke ci gaba da aiki - nan mutane a ranar Jajiberen Sabuwar Shekara na karanta sakamakon karshe na zagaye na biyu na zaben da ya kai tsohon fitaccen dan kwallon duniya George Weah ga nasara a Monrovia.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A dai wannan rana ce, aka dauki hoton wani karamin garken shanu suna shan iska a kan yashi a tsibirin Zanzibar na kasar Tanzania.

Labarai masu alaka