Rashin gamsuwa da girman nono 'na tauye gano cutar daji'

Woman self-examining breast Hakkin mallakar hoto Getty Images

Matan da ba su gamsu da girman nonuwansu ba, na da karancin yiwuwar dudduba lafiyar kansu don gano alamomin cutar daji, a cewar wani nazari.

Nazarin, wanda aka wallafa a wata mujalla mai suna Body Image, ya bibiyi rayuwar matan Burtaniya 384.

Binciken ya gano cewa wadannan mata ba su cika samun karfin hali su duba kansu don gano wani sauyi a nonunansu ba, kuma sukan yi jinkirin zuwa ganin likita idan sun gano wani sauyi.

Bincikar nonunansu "ka iya janyo wani tunani maras dadi kamar jin kunya da tozarta kai", in ji masu nazarin.

Akasarin matan da aka bibiyi rayuwarsu na nuna rashin gamsuwa da girman nonnansu:

  • 31% na son kananan nonuna
  • 44% na son manyan nonuna

Akasarin cutar daji

Kashi daya cikin uku na matan da aka binciki lafiyarsu, ba su cika ko ma sam ba sa binciken lafiyar mamansu.

Hukumar Inshorar lafiya ta Burtaniya na shawartar mata su tabbatar sun san yadda galibi siffar nonunansu take da kuma irin taushinsa a lokuta daban-daban cikin wata guda, ta yadda za su kwan da sanin duk wani sauyi da za a samu.

Sankarar mama ita ce cutar daji da ta fi zama ruwan dare a Burtaniya, inda ake duba lafiyar mata fiye da 55, 000 duk shekara.

Daga cikin matan da aka bincika, 55% sun ce za su so zuwa ganin likita da zarar sun gano wani sauyi a nononsu.

Sai dai, daya a cikin mata guda 10 da aka bibiya na son jinkirta zuwa ganin likita ko ma ba za su je ganin likitan ba gaba daya.

Cutar dajin da aka gano da wuri, galibi ta fi saukin magani da ma yiwuwar warkarwa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Alamomin cutar dajin mama da ake duddubawa

Farfesa Viren Swami, ta Jami'ar Anglia Ruskin, wadda ta gudanar da binciken ta ce: "Ga matan da ba su gamsu da girman nonunansu ba, irin wannan bincike ka iya zama wata barazana ga surar jikinsu don haka suna iya gujewa yin hakan.

"Bunkasa wayar da kai game da lafiyar mama ka iya zama abu mai matukar amfani wajen taimaka wa mata don su rika ganin mamansu a matsayin wani abu mai muhimmancinsa ga lafiya, maimakon abin kwalliya tsagwaro."

Dany Bell, daga Cibiyar Tallafa wa Masu Cutar Daji ta Macmillan, ta ce: "Rashin gamsuwa da tsarin surar jiki bai kamata ya hana mutane yin irin wannan bincike mai matukar amfani ba.

"Kullutu a mama alama ce ruwan dare ta cutar dajin nono, don haka dudduba nonon lokaci-lokaci na nufin gano matsalar tun tana karama."

Ya ce abu ne mai muhimmanci ga maza da mata su rika dudduba kansu.

Sophia Lowes, ta Cibiyar Binciken Cutar Daji ta Burtaniya ta ce yana da muhimmanci mata su kwan da sanin yadda siffar mamansu take da kuma irin taushinsa ta yadda za su lura da duk wani sauyi.

"Idan kun ga wani abu ba sabon ba, ku fada wa likitanku," ta ce.

"A lokuta da dama ba cutar daji ba ce - amma idan ita ce, gano ta da wuri ka iya zama wani abu mai muhimmanci."

Labarai masu alaka