Ina nan a kan bakana —Wenger

Hukumar ta Ingila ta bai wa Arsenal Wenger zuwa yammacin Juma'a, domin ya kare kansa.
Image caption Hukumar ta Ingila ta bai wa Arsenal Wenger zuwa yammacin Juma'a, domin ya kare kansa.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce babu abin da ya sauya dangane da kalaman da ya yi game da alkalan wasa, kuma yana nan a kan bakansa dari bisa dari.

An bukaci Wenger ya mayar da martani ga hukumar FA game da kalaman da ya yi wa alkalan wasa kafin da kuma bayan karawarsu da Chelsea ranar Laraba, a wasan da suka kunnen doki.

Wenger ya razana game da tuhumar da aka yi mishi bisa yin kalaman batanci, bayan da suka tashi wasa da West Brom.

Hukumar ta Ingila ta bai wa Arsenal Wenger zuwa yammacin Juma'a, domin ya kare kansa.

Wenger ya shaida wa manema labarai cewa,"Daga abin da na gani da kuma wanda na ji a dakin sanya kaya, na yi matukar razana da mamaki da cewa ana tuhumata."|

Labarai masu alaka