Hanyoyi bambarakwai 13 na sa yara barci

New year and knackered? Please, please go to sleep... Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sha shagulgulan Sabuwar Shekara an gaji ko? To a je a yi barci mana...

An sha gajiya bayan bukukuwan Sabuwar Shekara? Ko kina kwadayin karin 'yan sa'o'i don yin barci ki more? Ke uwa ce wadda rashin barcin 'ya'yanta ya sanya ta shafe tsawon dare ba rintsawa?

An yi ikirarin cewa kwanakin farkon watan Janairu su ne mafi wahalarwa ta fuskar raguwar barci.

Ma'auni na zamani dai shi ne adadin masu neman mafita a manhajar Google wadda ke nuna cewa jimlar "yarona ya ki barci ko child won't sleep" ta cilla sama a wannan lokaci cikin fadin duniya.

Kina iya kwatanta 'yan yatsu a gajiye na lallatsa wadannan kalmomi a kan wayar salula cikin tsakiyar dare, da fatan samun amsa.

Fatalwar Sabuwar shekara

Kananan yara na mayance wa kwamfyuta. Suna shafe tsawon dare ba tare da barci ba, suna wasannin kwamfyuta da halartar walima don haka damar yin barci tana kara raguwa sosai.

Su ma manya kamar yaran suna fama da irin wannan wahala. Farkon watan Janairu, babban lokaci ne da ake neman barci ido rufe.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Halartar bukukuwan walima a lokacin kirsimeti na da duk sigogin gajiyar da mutum

Sai dai idan gumu ta yi gumu. Uwayen da ke fama da rashin barcin 'ya'yansu, na bullo da dabarunsu na kar-ta-kwana.

Manhajojin bincike kan barci na Moshi Twilight Sleep Stories da calm.com, a baya-bayan nan an gano cewa suna daga cikin dabarun ba-sabon-ba da ake amfani da su.

Hanyoyi bambarakwai 13 na tarairayar yara su yi barci

 • Yi wa yaro bayani a kan tsare-tsaren samar da ababen more rayuwa na shugaban China, Xi Jinping
 • Sanya muryar da aka nada na babin wani littafin nazarin tattalin arziki na mutanen Scotland tun karni na 18, wanda wani malami mai gunduraswa ya karanta
 • Kallon wasan bidiyo mai rikitarwa na jirkita kalmomi
 • Sauraron wani sautin mutane da aka nada suna hamma tsawon sa'a daya
 • Kunna na'urar share daki ta zamani
 • Kallon wani fim mai tafiya cikin sanda na wasu tumaki da ke kiwo
 • Kirkirar wata siffar tunani kamar "Dodon gona", wanda yake kama duk yaran da ya tarar har bayan karfe 8 na dare ba su yi barci ba
 • Kwantar da yaro a kan kirji, a lokacin da uwa ke juya jikinta cikin da'ira a hankali
 • Sanya su cikin mota a tuka
 • Rera taken kasa baki a gumtse
 • Juya gadon yaro ya kalli wata kusurwa daban
 • Sanya agogo mai tsinke da ke fitar da sautin tik, tik, tik a kasan matashin yaro, don kwaikwayon bugun zuciyar mahaifiya
 • Sanya tufafi a kan gadon yaro suna kamshin jikin mahaifiya
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Idona biyu garau a shirye nake da aikin yau.

Labarai masu alaka