An hana musabaha a coci-coci

An haramta yin musabaha musamman a coci-coci a kokarin da ake yi na hana yaduwar cutar kwalara Hakkin mallakar hoto Dan Kitwood
Image caption An haramta yin musabaha musamman a coci-coci a kokarin da ake yi na hana yaduwar cutar kwalara.

Rahotanni daga Zambia na cewa an haramta yin musabaha musamman a coci-coci, a kokarin da ake yi na hana yaduwar cutar kwalara.

Har ila yau kuma hukumomi a birni Kitwe sun haramta sayar da danyen abinci da suka hada 'ya'yan itatuwa da kayan lambu a kan tituna.

Shugabanni gwamnati da limaman coci ne suka yanke shawarar hakan ne bayan da aka samu sama da mutum 2,000 sun farke da cutar kwalara a fadi kasar, tare da mutuwar gommai a babbban birnin kasar Lusaka.

Birni Kitwe mai nisan mil 200 daga arewacin Lusaka na kokarin kaucewa faruwar hakan.

Dokar za ta ci gaba da aiki har sai lokacin da komai ya daidaita, a cewar wata jaridar kasar.

Labarai masu alaka