Buhari ya ba da umarni a cire matattun da ya bai wa mukamai

A watan Oktoba ne Shugaba Buhari ya bayyana takaicin jinkirin nadin mambobin kwamitocin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Oktoba ne Shugaba Buhari ya bayyana takaicin jinkirin nadin mambobin kwamitocin gudanarwa na hukumomin gwamnatin tarayya

Fadar shugaban Nigeria ta ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya bayar da umarni a cire sunayen matattun da ke cikin wadanda ya nada kan mukamai.

Shugaban ya bukaci sakataren gwamnatin tarayyar kasar Boss Mustapha ya cire sunayen matattun sannan ya sake yin garambawul kan sunayen da ke cikin mutanen da aka nada kan mukaman.

Bai bai wa shugaban kasar shawara kan shafukan sada zumunta, Mallam Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa tuni mutanen da Shugaba Buhari ya dora wa alhakin gudanar da wannan aiki suka yi nisa a cikinsa kuma nan gaba kadan za su mika masa rahotonsu.

A kwanakin baya ne shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da sunayen mutum 209 da mambobi fiye da 1,250 domin su jagoranci hukumomin wasu ma'aikatun gwamnati.

Amma sai aka ga sunayen wasu matattun 'yan Najeriya cikin wadanda aka nadan.

Wannan al'amari ya janyo martani a tsakanin 'yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

Amma sai aka ga sunayen wasu matattun 'yan Najeriya cikin wadanda aka nadan.

Wannan al'amari ya janyo muhawara a tsakanin 'yan Najeriya musamman a shafukan sada zumunta.

Sai dai kakakin shugaban kasar Malam Garba Shehu ya ce babu dalilin da zai sa a dauki matakin ladabtarwa a kan wadanda suka yi kuskuren fitar da sunayen.

Ya fada wa BBC cewa an shirya wannan jerin sunayen ne fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Ya kuma bayyana cewa, "Tun watan Oktobar shekarar 2016 aka rubuta sunayen, amma sai aka ajiye shi domin sukar da wasu gwamnoni suka yi."

Ya kare gwamnati daga zargin rashin iya aiki.

Kakakin gwamnatin ya ce bai ga dalilin da za a dauki matakin ladabtarwa akan wadanda suka saki sunayen ba.

"Babu wani dalilin da za a dauki mataki akan wani jami'in gwamnati saboda wannan kuskuren," inji shi.

A cikin sunayen akwai sunan Sanata Francis Okpozo wanda ya mutu a watan Disambar 2016, amma sai ga sunansa a cikin nadaddun.

An nada shi ya shugabanci hukumar Nigeria Press Council.

Ban da shi akwai Donald Ugbaja, wani tsohon mataimakin sufeto-janar na 'yan sandan Najeriya wanda ya mutu a farkon wannan shekarar, wanda aka nada shi domin ya shugabanci hukumar Consumer Protection Council.

Akwai kuma marigayi Rabran Christopher Utov, wanda sunansa ya fito a jerin sunayen mambobin hukumar Nigeria Institute of Social and Economic Research.

Garba Shehu ya ce za a sauya sunayen matattun mutanen da na wasu 'yan kasar da suka cancanta.