Me ya ja hankalin mazan Thailand suke yi wa mazakuta bilicin?

Lokacin da ake yi wa wani aikin tiyatar bilicin din a asibiti Hakkin mallakar hoto LELUXHOSPITAL
Image caption Sauya launin fata ba sabon abu ba ne a tsakanin mutane, amma yi wa al'aura bilicin abu ne sabo

Wata sabuwar al'ada da maza da mata ke yi wa al'aurarsu bilicin a kasar Thailand tana ta bazuwa a cikin kwanakin nan, lamarin da ake ganin kamar salon neman kyau a kasar na neman wuce gona da iri.

Shafe-shafen mai domin mutum ya yi fari ko ya kara haske ba wani sabon abu ba ne a Asia da sauran kasashe da dama, inda kusan ake danganta baka ko duhun fata da yawan aikin wahala, da kuma talauci.

A sabo da haka ne a lokacin da aka sanya hoton bidiyon wani sabon aiki da ake yi a wani asibiti inda ake yi wa azzakarin maza bilicin domin ya yi haske ko fari, hoton ya yi ta bazuwa a intanet din kamar wutar daji.

Hoton bidiyon aikin wanda aka sanya a Facebook daga asibitin da yake abin ta hanyar amfani da wata na'ura ta musamman da lantarki ya rage sinadarin da ke sa fata baki (melanin), cikin kwana biyu kawai ya ba zu tsakanin mutane sau sama da 19,000.

Hoton bidiyon yana dauke da cikakken bayani da hotuna daga dakin tiyatar na yadda ake aikin da kuma yadda azzakarin mutun ke kasancewa fari bayan aikin.

Babban jami'in tallata ayyukan asibin (Lelux Hospital) da ke aikin, Popol Tansakul ya gaya wa BBC cewa wata hudu da ya wuce ne suka bullo da aikin yi wa al'aurar mata bilicin, farjin ya zama fari tas ba wata bakar fata.

Ya ce daga nan ne kuma sai mutane suka rika neman a bullo musu da yadda su ma maza za a rika yi musu bilicin din a azzakarinsu, a kan aka ne suka fito na mazan wata daya da ya wuce.

Jami'in ya ce ana biyan asibitin dala 650 ko fam 480 kwatankwacin naira 234,720 a aikin da suke yi kashi biyar.

Mista Popol ya kara bayani da cewa abin ya fi karbuwa a tsakanin 'yan luwadi da madigo da kuma 'yan daudu, wadanda ke kula sosai da al'aurarsu, saboda suna son ko ina a jikinsu ya zamanto da yana da kyau.

Hakkin mallakar hoto LELUXHOSPITAL
Image caption Hukumomin kasar ta Thailand na gargadin mutane a kan hadarin yin aikin ga farjin mutum na gaba

A yanzu asibitin na samun maza da mata akalla 20 zuwa 30 a duk wata da ke zuwa a yi musu aikin, inda wasu ke tasowa tun daga Myanmar da Cambodia da kuma Hong Kong.

Ana dai ta samun masu yabo da kuma masu suka a kan abin, inda wata mata ta ce ita ba launi ba ne ya dame ta, abin da yake da muhimmanci a wurinta shi ne girma da kuma karfin mazakutar kawai.

Tuni ma'aikatar kula da lafiya ta kasar ta Thailand ta fitar da gargadi kan aikin yi wa al'aurar bilicin, da cewa zai iya haddasa wata matsala ga masu yi a nan gaba, kamar ta tabo ko lalacewar fata ko mahaifa da zafi a al'aurar ko kuma matsala wajen yin jima'i.

Ma'aikatar lafiyar ta ce idan mutum ya daina yin bilicin din a al'aurar a can zai sa ainahin launin fatar ya dawo, wanda hakan kuma zai sa a ga wurin ya yi dabbare-dabbare, ba kyawun gani.