Nigeria: Ba mu muka nada wa Buhari matattu ba —APC

Shugaba Buhari ya umarci sakataren gwamnatinsa, Boss Mustapha ya cires sunayen matatu daga cikin jerin sunayen wadanda gwamnatinsa ta bai wa mukamai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Buhari ya umarci sakataren gwamnatinsa, Boss Mustapha, ya cire sunayen matatu daga cikin jerin sunayen wadanda gwamnatinsa ta bai wa mukamai

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ce ba ita ta saka sunayen matattu cikin jerin sunayen wadanda shugaban ya fitar a nade naden da ya yi na baya bayan nan ba.

A wata ganawar da shugaban jam'iyyar APC , Cif Odigie Oyegun, ya yi da manema labarai ranar Asabar, shugaban jam'iyyar ya ce jam'iyarsa ba ta da laifi a nade naden da gwamnatin Buhari ta yi inda aka saka sunayen matattu a cikin wadanda aka nada.

A kwanakin baya ne Shugaba Muhammadu Buhari ya fitar da sunayen mutum 209 da mambobi fiye da 1,250 ta ofishin sakataren gwamnatinsa, Boss Mustapha, domin su jagoranci hukumomin wasu ma'aikatun gwamnati.

Bayan shugabn ya fitar da sunayen ne dai aka fara ganin sunayen wadanda suka mutu a cikinsu, lamarin da ya janyo ce-ce-kuce.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Odigie Oyegun ya ce jam'iyyar ba ta yi laifi ba a nade naden matattu da gwamnatin Buhari ta yi

Yayin da wasu suka soki gwamnatin Shugaba Buhari da sakaci, wasu kuwa uzuri suka nema wa gwamnatinsa suna masu cewa sabida an dade da tattara sunayen wadanda aka nada ne ya sa aka samu matattu a cikinsu.

Shugaba Buhari dai ya bukaci sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Boss Mustapha, ya cire sunayen matattau daga cikin wadanda aka nada a nade naden da suka janyo ce-ce-kuce.

Cif Oyegun ya ce jam'iyyar tana da hannu a wajen tattara sunayen wadanda aka nada din daga farko, amma ba a tuntunbe ta ba daga karshe, lamarin da ya sa jerin sunayen ya bar baya da kura.

Shugaban APC din ya ce tun farko fara mulkin gwamnatin ne jam'iyyar ta sa shugabannin jam'iyar na jihohi su kawo sunayen wadanda za a nada a mukamai kuma ta mika sunayen ga gwamnati.

Ya kara da cewar kafin a fitar da sunayen wasu sun sauya jam'iyya yayin da wasu suka mutu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jam'iyyar APC ta ce da an tuntube ta daga farko da ba za a sami kuskuren da aka samu a cikin jerin sunayen da aka fitar ba

Shugaban jam'iyyar APC din ya ce ya kamata dai fadar shugaban kasar ta tuntunbi jam'iyyar duk lokacin da za ta yi irin wadannan nade naden a gaba domin gudun irin wadannan kurakuran.

Labarai masu alaka