Wa ya kama shugaban 'yan a-waren Cameroon a Nigeria?

Masu fafutuka suna bukatar gwamnatin Najeriya ta yi bayani game da abin da ya sami shugabansu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Masu fafutuka suna bukatar gwamnatin Najeriya ta yi bayani game da abin da ya sami shugabansu

Kungiyar da ke fafutukar ballewar kudancin Kamaru ta ce jami'an tsaro sun kama shugabanta tare da akalla mutum shida a birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

An kama Julius Ayuk Tabe, wanda shi ne shugaban kungiyar da ke neman 'yancin yankin Ambazonia, tare da mutum shida ranar Juma'aa cikin wani otel a birnin Abuja.

Kungiyar da ke fafutukar ballewar yankin Ambazonia ta ce an kama su ne a lokacin da suke son su fara wani taro kan 'yan gudun hijirar da suka tsere Najeriya daga kudancin Kamaru domin tashe-tahsen hankulan da ake fama da su a yankin.

Hakkin mallakar hoto @GovAmba -Twitter
Image caption Tun ranar 1 ga watan Oktobar 2017 da kungiyar ta ayyana ballewar yankin daga kasar ne tashe tashen hankula suka karu a kudancin Kamaru

Kawo yanzu dai babu tabbacin abin da ya sa aka kama mutanen yayin da wata majiya ta shaida wa BBC cewa 'yan sandan farin kaya sun kama mututanen ne domin takardun zamansu a Najeriya sun gama aiki.

Sai dai kuma wasu masu fafutuka sun ce kamun nasu na da alaka da siyasa domin yawancin 'yan kungiyar da ke fafutukar neman 'yancin yankin Abazonia masu neman mafakar siyasa ne, abin da ke nufin cewa ba sa bukatar takardu domin su ci gaba da zama a cikin kasar.

A halin yaznu dai masu fafutukar da ke neman ballewar kudancin Kamaru suna bukatar gwamnatin Najeriya ta yi bayani game da abin da ya sami shugabansu yayin da wasu ke zargin jami'an tsaron Kamaru da kama mutanen a Abuja.

Kafin dai a kama wadannan mutanen, mutanen da suka tsere daga Kamaru zuwa Najeriya domin rikicin da ake yi a kudancin Kamaru din sun wuce dubu 28,000.

'Yan gudun hijirar da suka shigo Najeriyar dai sun shiga garuruwa da jihohi daban-daban ne a kasar ciki har da Abuja da Legas da Inugu da Binue da Akwa Ibom da kuma Cross River.

Hakkin mallakar hoto Eric Shu
Image caption Abinci da muhalli da kuma magani su ne muhimman kalubalen da 'yan gudun hijirar ke fuskanta

Majalisar Dinkin Duniya dai ta yi gargadin cewa za a sami karin dubban 'yan gudun hijira da za su shigo Najeriya daga Kamaru idan rikicin ya ci gaba.

Labarai masu alaka