Za mu ci gaba da kai wa Myanmar hari—Mayakan Rohingya

An aerial view showing the burnt-out village near Maungdaw township in Rakhine State, western Myanmar, 27 September 2017 Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A shekarar da ta gabata, jami'ai sun zargi mayakan kungiyar Arsa da kauyen mabiya addinin Hindu mai suna Yebawkyaw tare da jashe da yawa daga cikin mabiyanta

Wata kungiyar masu tayar da kayar baya wacce ta fito daga cikin tsiraru 'yan kabilar Rohingya a Myanmar ta ce za ta ci gaba da yakar gwamnatin kasar.

Hare-hare da kungiyar Arakan Rohingya Salvation Army (ko Arsa a takaice) ta kai a shekarar da ta gabata ce ta haddasa ramakon gayyar da ta raba kimanin 'yan kabilar Rohingya 650,000 da muhallansu, lamarin da ya sa suka tsere zuwa Bangladesh.

Kungiyar ta ce ita ta yi wa wata motar sojoji kwanton bauna a jihar Rakhine ranar Juma'a inda mutum uku suka ji rauni.

Kungiyar da gwamnatin kasar take yi wa kallon kungiyar ta'addanci, ta ce tana fafutukar neman hakkokin 'yan kabilar Rohingya ne.

Su waye ne 'yan kungiyar Arsa?

Arsa tana harkarta ne a jihar Rakhine da ke arewacin Myanmar, wurin da mutanen Rohingya suka fuskanci cin-zarafi . Gwmnatin Myanmar ta hana su hakkin zama 'yan kasa, kuma tana yi musu kallon bakin haure da suka shigo kasar daga Bangladesh.

Rikici na barkewa tsakanin kabilu daga lokaci zuwa lokaci , amma a shekarar da ta gabata ,rikicin 'yan kabilar Rohingya masu makamai ya ta'azzara.

Hakkin mallakar hoto Youtube
Image caption Kungiyar ta fitar da wani sakon bidiyon da ya nuna shugabanta a watan Agusta

Kungiyar Arsa tana kaddamar da hare-hare ne jifa-jifa, sai dai ranar 25 ga watan Agustan shekarar da ta gabata ta kaddamar da hare-hare kan shingayen sojoji da 'yan sanda 30, lamarin da ya janyo matakin soji mai tsauri.

Labarai masu alaka