Liverpool na neman Riyad Mahrez

Riya Mahrez yana daya daga cilkin 'yan wasan da Liverpool ke hako Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Riya Mahrez yana daya daga cilkin 'yan wasan da Liverpool ke hako

A lokacin da Barcelona ta dauke mata Philippe Countinho, kungiyar kwallon kafa ta Liverpool tana neman 'yan wasan da za ta saya.

Daya daga cikin 'yan wasan da kungiyar ke hako shi ne Riyad Mahrez na Leicester City.

Ana tsammanin za a gwada lafiyar dan wasan mai shekara 26 a Liverpool ranar Lahadi, in ji Bein Sports.

Labarai masu alaka