Yadda muka kashe 'mai garkuwa da mutane' a Fatakwal— Sojoji

Za a mayar da gawar Don Waney Fatakwal na jihar Rivers inda za a mika ta ga rundunar 'yan sandan jihar.
Image caption Za a mayar da gawar Don Waney Fatakwal na jihar Rivers inda za a mika ta ga rundunar 'yan sandan jihar.

Runduna ta shida ta sojin Najeriya a Fatakwal ta bayar karin haske game da yadda ta kashe mutumin da ake zargi da kasancewa sanannen shugaban kungiyar asiri da ke yin garkuwa da mutane da kuma yi musu kisan gilla.

A wata sanarwar da rundunar ta fitar kuma kanar Aminu Iliyasu ya sanya wa hannu, rundunar ta ce ta samu sahihin bayani ne daga mutanen gari game da mabuyar Don Waney wanda ake zargi da kitsa harin da ya kashe mutum 23 dake dawowa daga coci a ranar farkon shekarar 2018 a garin Omoku na jihar Ribas.

Rundunar ta ce a lokacin da sojoji suka kai mabuyarsa sun sami abubuwa masu tayar da hankali kamar su makamai ir-iri da nakiya da kayan sarki da kwarangwal goma da sauransu.

Sanarwar ta ce bayan ya kashe mutanen da ke dawowa daga coci ranar farkon shekarar 2018, binciken jami'an tsaron farin kaya ya nuna cewa Don Waney ya koma garin Inugu ne inda ya fara zama cikin mutane.

Sai dai kuma sanarwar ta ce bayanan da jami'an tsaro suka tattara ya nuna cewa Don Wayne yana shirin sake kaddamar da hari kan garin Omoku daga Inugun.

Kafin ya kaddamar da harin dai, jami'an tsaro na farin kaya sun gano inda ya ke a garin na Inugu.

Bayan an gane inda yake ne sojoji daga runduna ta 82 da ke Inugu da kuma jami'an tsaro na farin kaya daga jihar Ribas suka yi wa inda yake dirar mikiya.

Da Don Weyne da mataimakinsa (Ikechukwu Adiele) da kuma wani dan kungiyarsu (Lucky Ode) suka ga an kusa kama su, sai suka nemi tserewa ta kofar bayan gidan da suke.

Wannan ne ya sa dakarun da suka kai samamen suka harbe su, in ji sanarwar.

Za a mayar da gawar Don Waney Fatakwal na jihar Rivers inda za a mika ta ga rundunar 'yan sandan jihar.

Labarai masu alaka