Uwar da za ta sayar da tagwayenta za ta fuskanci hukunci

A watan jiya ne aka kama ta a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya
Image caption A watan jiya ne aka kama ta a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya

An yanke wa wata mata da ta yi yunkurin sayer da 'ya'yanta tagwaye 'yan wata daya hukuncin daurin wata 10 a gidan yari, ko kuma ta biya tarar naira dubu 10 don kaucewa daurin.

A watan jiya ne aka kama ta a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya, bayan da ta yi yunkurin sayar da yaran a kan kudi naira 350,000.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Alkali Nuradeen El-Laden ya ce ya zabi ya saukaka wa matar hukuncin ne, saboda tsoron lafiyar jariran.

Har ila yau wasu rahotanni na cewa alkalin ya sassauta ne saboda ya fahimci matar ta yi yunkurin sayar da jariran ne sakamakon "bakin talauci" da take fama da shi, tare da nuna nadamar abin da ta aikata.