Jaruman Hollywood sun goyi bayan wadanda a ka yi wa cin zarafi

Da yawa daga cikin jaruman sun halarci bikin tare da masu fafutukar daidaito tsakanin jinsi da launin fata Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Da yawa daga cikin jaruman sun halarci bikin tare da masu fafutukar daidaito tsakanin jinsi da launin fata

A yau ne a ke bikin bayar da lambar yabo na Golden Globes a birnin Los Angeles a Amurka, inda wasu mahalarta bikin kuma jaruman fina-finan Hollywood su ka sanya bakaken kaya don nuna goyon baya ga wadanda su ka fuskanci cin zarafi.

Da yawa daga cikin jaruman za su halarci bikin ne tare da masu fafutukar daidaito tsakanin jinsi da launin fata domin nuna tasirin matsalar.

A baya bayan nan dai, an zargi mai shirya fina-finai Harvey Weinstein da cin zarafin mata da dama, inda hakan ya janyo zarge-zarge a kan wasu jarumai da kuma wasu masu fada a ji a Hollywood din.

Labarai masu alaka