An kama 'yan makarantar sakandare masu 'cikin-shege'

Rahotanni sun ce ana samun karin 'yan mata masu ciki a Hakkin mallakar hoto AFP

Masu fafutukar kare hakkin yara sun soki kamen da aka yi wa 'yan makaranta masu ciki da iyayensu a karshen mako.

An kama yaran makarantar sakandare 'yan kasa da shekara 20 a Tandahimba, da ke arewacin Tanzaniya, bisa umarnin wani kwamishina na gundumar kuma aka bayar da belinsu daga baya.

Kafar watsa labarai ta Citizen ta ambato masu fafutukar kare hakkin yara da na jinsi suna cewa ya kamata hukumomi su kama mazajen da suka yi wa matan ciki maimakon wadanda aka yi wa cikin.

Hukumomi suna neman mazajen da suka yi wa 'yan matan ciki, in ji Mohamed Azizi, wani jami'in gundumar da kafar watsa labaran ta ambato.

An ambato Mista Azizi yana cewa kamen yana cikin kokarin da ake yi domin kawo karshen cikin 'yan makaranta a yankin inda rahotanni suka ce 'yan makaranta 55 sun yi ciki cikin shekaru biyun da suka gabata.

Siyasar yankin ta mayar da hankali kan cikin yara 'yan kasa da shekara 20 cikin a kwanakin nan.

A karshen shekarar da ta gabata ne aka yin Allaha-wadan Shugaban Tanzaniya, John Magufuli kan kalaman da ya yi cewa kar a yarda 'yan matan da suka haihu su koma makaranta.

Labarai masu alaka