Kun san mutum nawa aka kashe a mako daya a Nigeria?

Jami'an tsaro sun kashe mutumin da ake zargi da hannu a kisan mutane a Fatakwal Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jami'an tsaro sun kashe mutumin da ake zargi da hannu a kisan mutane a Fatakwal

Kusan mutum dari daya ne suka mutu a hare-haren da aka kai a sassan Najeriya daban-daban tun daga ranar karshe ta 2017 zuwa karshen makon jiya.

Idan muka soma daga jihar Ribas da ke kudu maso kudancin kasar, 'yan bindiga sun kashe mutum 23 bayan sun fito daga coci inda suka je addu'o'in murnar sabuwar shekara.

Lamarin ya abku ne a garin Omoku da ke karamar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni, mai nisan kilomita 85 daga birnin Fatakwal, babban birnin jihar.

Rundunar 'yan sandan jihar dai ta tabbatar wa BBC da abkuwar lamarin.

Wasu rahotanni na cewa harin yana da nasaba da rigingimu da ake yi tsakanin wasu gungu da ba sa ga maciji da juna a yankin Naija Delta mai arzikin man fetur.

Kuma a ranar Lahadi ne Runduna ta Shida ta sojojin kasa a Najeriyar da ke Fatakwal ta ce ta kashe mutumin da ake zargi da hannu a kisan mutanen.

A wata sanarwar da mai magana da yawunta Kanar Aminu Iliyasu ya fitar, rundunar ta ce ta samu sahihin bayani ne daga mutanen gari game da maboyar Don Waney, wanda ake zargi da kitsa harin.

Benue

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fulani makiyaya sun musanta zargin

Kazalika a dai ranar karshe ta shekarar 2017, wasu mutane da ake zargi Fulani makiyaya ne suka soma kai hari a wasu kauyuka na jihar.

Gwamnatin jihar ta Benue dai ta ce an kashe akalla mutum 33 a hare-haren da aka kai kauyukan jihar da ke karamar hukumar Guma, mahaifar gwamnan jihar.

Kwamishinan watsa labarai na jihar, Lawrence Onoja, wanda ya tabbatar wa BBC adadin mutanen da aka kashe, ya kara da cewa an fara kai hare-haren ne ranar karshe ta shekarar da ta gabata kuma aka ci gaba da kai wa har zuwa safiyar Talata ta makon jiya.

Sai dai kungiyar Miyetti Allah ta bakin shugabanta Ubbi Haruna ta shaida wa BBC cewa ba Fulani makiyaya ne suka kai harin ba, tana mai zargin gwamnatin jihar da kashe Fulanin da ke kan hanyarsu ta ficewa daga jihar a lokacin.

Hare-haren da aka kai a Rivers da Benue sun sa 'yan kasar, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta, sun yi ta sukar gwamnatin tarayya.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya bayyana takaicinsa kan lamarin sannan ya umarci Babban Sufeton 'yan sandan kasar ya karfafa tsaro a yankunan.

Hakan ne ma ya sa aka aike da manyan jami'an rundunar 'yan sanda jihohin domin su wanzar da zaman lafiya.

Gamboru

Da asubahin ranar uku ga wannan watan ne kuma wani dan kunar bakin wake ya kai hari wani masallaci a garin Gamboru da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Ganau sun tabbatar wa BBC cewar harin ya kashe akalla mutum goma ciki har da maharin.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin.

Sai dai kuma shugaban wani bangare na kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya yi dauki alhakin kai wasu hare-hare a wani bidiyon da ya fitar ranar Talata.

Taraba

A karshen makon jiya kuma, an kai hari a kauyen Rhobi na karamar hukumar Lau da ke jihar Taraba.

Wani mazaunin yankin Felix Manthly ya shaida wa BBC cewa, "Wasu mutane ne da ake zargin Fulani ne suka kai harin da yin harbe-harbe da kuma cinna wa gidajen jama'a wuta. Amma wadannan Fulanin kamanninsu daban da na wadanda muka saba gani.

"Yanzu haka muna da mutane 25 da aka kashe ban da wadanda suka gudu amma aka bi su a kan mashin aka harbe".

Kungiyar Miyetti Allah a Najeriya ta ce ba Fulani ne suka kai harin ba.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin shugaban reshenta na jihar Lagos, Alhaji Abdullahi Lele.

"Bata musu suna ake yi. Don wasu ne ke shigar Fulani suna ta'addanci, sai a ce Fulani ne", in ji shi.

Ya kara da cewa: "Saboda rashin kaunar da ake nuna wa Fulani a Najeriya, duk inda suke a takure suke".

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar David Misal ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin, sai dai ya ce mutanen da aka kashe ba su da yawa.

'Yan Najeriya da dama dai na ci gaba da kira ga shugaban kasar da ya dauki matakin gaggawa na ganin ba a ci gaba da irin wadannan kashe-kashe ba.

Labarai masu alaka