Malaman makarantun Kaduna sun bijirewa El-Rufai

Kaduna
Image caption A sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar game da yajin aikin, ta yi barazanar daukar mataki mai tsauri kan duk malamin da ya ki fitowa kan aikinsa.

Malaman Makarantun firamare da sakandare sun soma yajin aikin sai baba ta gani a jihar Kaduna arewacin Najeriya.

Kungiyar Malamai ta kasa NUT ce ke jagorantar yajin aikin da aka soma a yau Litinin domin adawa da matakin gwamnatin jihar na korar Malaman Firamare 22,000.

Wakilin BBC Nura Muhammed Ringim ya ce makarantu sun kasance a rufe, bayan da malamai suka kauracewa aji a yau Litinin da daliban ya kamata ace sun koma makaranta bayan hutun kirsimeti da sabuwar shekara.

Ya ce kungiyar Malaman ta bi makarantu a sassan jihar tana kafe sanarwar shiga yajin aikin.

Tun da farko kungiyar Malaman ta ba gwamnati wa'adin mako biyu kan ta janye matakin korar malaman kafin shiga yajin aikin, wanda ya shafi makarantun Firamare da Sakandare.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta jarraba malaman firamare guda 33,000, amma 66 bisa 100 ne gwamnatin ta ce suka fadi jarabawar.

A watan Disemban da ya gabata kotun ma'aikata ta kasa ta ba gwamnan jihar Nasir El- Rufa'I umurnin dakatar da matakin korar malaman.

Amma tuni gwamnatin ta aike da takardar sallama ga malaman da suka fadi jarrabawar da aka shirya mu su ta matakin 'yan aji hudu don jarraba kwazonsu.

Hakkin mallakar hoto KADUNA STATE GOVERNMENT
Image caption Gwamna El-Rufai ya ce zai hukunta wadanda suka tafi yajin aiki

Kuma a cikin sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar game da yajin aikin, ta ce ba gudu babu gudu ba ja da baya kan aniyar korar malaman tare da barazanar daukar mataki mai tsauri kan duk malamin da ya ki fitowa kan aikinsa.

Labarai masu alaka