Somaliland ta kafa dokar hana fyade a karon farko

Somaliland's rape act Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A baya ana matsa wa mutanen da ya yi fyade auren wadda ya yi wa aika-aikar

Somaliland da ta ayyana kanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta ta zartar da wata doka da ta haramta fyade a karon farko.

A baya dai, ana matsa wa matan da aka yi wa fyade da lallai su auri mutanen da suka yi musu wannan aika-aika kuma ala dole iyayenta su goyi bayan wannan kuduri don boye abin kunyar da ke tattare da fyaden.

A yanzu masu fyade suna iya fuskantar hukuncin dauri na akalla tsawon shekara 30 a gidan yari.

Shugaban majalisar dokokin Somaliland, Bashe Mohamed Farah, ya fada wa BBC cewa an samu karuwar aikata fyade don haka yana fata sabuwar dokar za ta taimaka wajen kawo karshen wannan al'amari.

Ya ce: "Muna ganin mutane suna aikata hatta fyaden gungu a baya-bayan nan".

"Babban abin da wannan sabuwar doka ke kokarin jaddadawa shi ne a kawo karshen fyade gaba daya.

Sabuwar dokar ta fara aiki ne bayan tsawon shekaru ana ta kamun kafa daga kungiyoyin kare 'yancin yara da mata.

Wata mai fafutukar kare hakkokin mata, Faisa Ali Yusuf ta ce sun yi ta jiran irin wannan doka tsawon lokaci.

Wakiliyar BBC Anne Soy ta ce dokar na zuwa ne daidai lokacin da Somaliland ke rawar jikin ganin ta samu kima zama kasa mai bin tsarin dimokradiyya da dokoki masu tasiri a idon duniya.

A shekarar 1991 ne ta ayyana kanta a matsayin kasa mai cin gashin kanta daga Somalia, sai dai ba ta iya samun karbuwa a matsayinta na kasa ba a tsakanin kasashe.

Wakiliyarmu ta ce har yanzu babu dokar da ke haramta yin fyade a Somalia.

Labarai masu alaka