Iran ta haramta koyar da harshen Ingilishi

Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya jima da nuna damuwa kan yadda ake koyar da harshen Ingilishi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya jima da nuna damuwa kan yadda ake koyar da harshen Ingilishi

Iran ta haramta koyar da harshen Ingilishi a makarantun Firamare na kasar inda ta ce harshen na gurbata al'adu.

Ma'aikatar ilimi ta kasar ta ce ta na fatan karfafa koyon harshen Farsi da kuma al'adun Musulunci na kasar ga daliban Firamare.

A kwanakin baya Jagoran addini a Iran Ayatollah Ali Khamenei ya nuna damuwa kan yadda ake koyar da harshen Ingilishi.

Ya bayyana matsayin nasa ne duk da cewa 'yan kasar da dama na ganin muhimmancin koyar da harshen Ingilishi.

Ba wajibi ba ne ga dalibai 'yan shekaru 12 su koyi Ingilishi a makarantun sakandare, sai dai wasu makarantu na koyar da harshen da wuri saboda karbuwar sa.

Sakatare a ma'akatar ilimi ta kasar Mehdi Navid-Adham ya shaidawa kamfanin dillacin labaru na kasar cewa ba a tilasta koyon harsunan kasashen waje a makarantun Firamare ba.

Ya kara da cewa makarantun Firamaren da ke koyar da Ingilishi a lokutan da aka ta shi daga karatu a makarantu sun karya doka.

Sai dai wannan haramcin bai shafi wasu makarantu masu zaman kansu ba da ke koyar da harsunan kasashen waje a matakin karatun sakandare.

Labarai masu alaka