Jirgin yaki da Boko Haram ya yi hatsari

Rundunar sojin saman ta ce babu asarar rai a hatsarin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar sojin saman ta ce babu asarar rai a hatsarin

Rundunar sojin sama ta Nigeria ta ce wani jirginta mai saukar angulu kirar Mi-17 da ke yaki da mayakan Boko Haram ya yi hatsari a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa, kakakin rundunar sojin saman AVM Olatokunbo Adesanya ya ce hatsarin ya abku ne ranar Litini kuma jirgin ya yi matukar lalacewa.

Sai dai rundunar sojin saman ta ce babu asarar rai a hatsarin.

Sanarwar ta kara da cewa babban hafsan sojojin sama na Nigeria Sadique Abubakar, ya bada umurnin kafa kwamitin bincike don gano musabbabin hatsarin.

Kakakin rundunar sojin saman ya ce kafa kwamitin ya yi daidai da tsarin da ake bi a kasashen duniya.

Rundunar sojin sama ta kuma bukaci hadin kai daga jama'a a kokarin ta na samar da tsaro da kare dukiyoyin 'yan kasar.

Labarai masu alaka