Budurwa ta kashe kanta don an hana ta soyayya da Musulmi a India

India Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mata na fuskantar cin zarafi a India

Wata budurwa mabiya addinin Hindu ta kashe kanta bayan ta fuskanci tsangwama kan soyayyarta da wani musulmi a jihar Karnataka da ke kudancin India.

Kafin ta kashe kanta ta fada wa kawarta ta kafar whatsApp cewa, ita tana son musulmai a yayin da ta ke fuskantar tsangwama kan soyayyarta da wani musulmi.

'Yan sandan India da suka tabbatar da lamarin, sun ce mutane sun ta rarraba hoton tattaunawar a kafofin sadarwa na intanet.

Burdurwar 'yar kimanin shekaru 20 ta kashe kanta ne a ranar da wasu gungun mutane guda biyar masu tsattsauran ra'ayin addinin Hindu suka yi wa iyayenta barazana a gidansu a ranar Asabar.

Da farko dai 'yan sanda sun ce kisan kai ne, amma bayan fadada bincike sun fahimci kafofin sadarwa na intanet ne suka taka rawa da har suka tursasawa budurwar kashe kanta.

K Annamalai, babban jami'in 'yan sanda a gundumar Chikkamagaluru, ya shaidawa BBC cewa budurwar ta rubuta wani dan karamin sako kafin ta kashe kanta.

"Ta ambaci cewa akwai hotonta tare da wani mutum wanda ba addininsu daya ba. Mutane sun fara tsokaci akai tare da sukar halayenta," a cewar shi.

Ya kara da cewa ta kashe kanta ne bayan wasu mutane biyar sun ziyarci gidansu kuma suka mika kokensu ga iyayenta cewa tana soyayya da musulmi.

Ya ce 'yan sanda sun cafke mutum daya, kuma suna ci gaba da bincike domin gano sauran.

'An yi asarar budurwa'

Wakilin BBC Imran Qureshi, wanda ya karanta tattaunawar, ya ce cikin lokaci kankani aka turawa mutane sakwannin hoton tattaunawar da aka dauka ta Whatsapp.

A cikin sakwannin an ba ta shawarar ta kaucewa yin soyayya da wani mutum mabiyi wani addini. Amma sai ta amsa cewa "ina son musulmai"

Ta kara da cewa ita ba ta ga wani laifin yin mu'amula da mabiyi wani addini ba.

Mista Annamalai ya ce "duk wanda ya kalubalanci budurwar, ko dai a Facebook ko WhatsApp za su kama shi".

Ya ce sun yi imanin tsangwama ce ta janyo aka yi hasarar rayuwar budurwar, Kuma yanzu sun dauki wannan lamari da muhimmaci domin sun fahimci ba laifinta ba ne.

An dade ana zaman doya da manja tsakanin mabiya addinin Hindu da Musulmi inda ake zargin maza musulmi da kulla soyayya da matan Hindu, abin da 'yan Hindun suka kira makircin 'jihadi a Soyayya'.

Labarai masu alaka