Kun san ranakun da za a yi zaben 2019 a Nigeria?

Hakkin mallakar hoto CHANNELS TV
Image caption INEC na so ta rika yin zabe a lokaci guda

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta fitar da jadawalin zaben kasar na shekarar 2019.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya shaida wa manema labarai hakan a Abuja, ya ce za a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu.

A cewarsa, za a yi zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jihohi da kuma na birnin tarayya ranar biyu ga watan Maris.

Farfesa Yakubu ya ce daga yanzu za a rika gudanar da zabukan ne a ranakun da aka ambata ba tare da an dage ko jinkira gudanar da su ba.

Ya ce za a kammala zabukan fitar da gwani da kuma warware korafe-korafen da za su biyo bayansu kafin ranar 18 ga watan Agustan 2018.

A shekarar 2019 ne dai INEC za ta gudanar da zabuka a karon farko a karkashin jagorancin Farfesa Mahmood Yakubu.

Ya karbi jagorancin hukumar ne bayan saukar Farfesa Attahiru Jega, wanda ya gudanar da babban zaben kasar na shekarar 2015, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.