Daure mashaya wiwi ba shi da alfanu — Obasanjo

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Obasanjo ya ce daure 'yan wiwi yana sa wa suna zama manyan masu aikata laifuka

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira a daina daure kananan mashaya wiwi, yana mai cewa hakan na mayar da su manyan masu aikata laifuka.

Cif Obasanjo ya shaida wa BBC cewa a lokacin da aka daure shi a gidan yarin Najeriya ya hadu da mutane da dama wadanda laifinsu bai wuce "kama su da kullin wiwi ba, amma aka daure su".

A cewarsa, "Idan matashi ya soma shan wiwi kuma aka kama shi aka daure a gidan yari bai fito a matsayin babban mai aikata laifi. Maimakon haka, ya kamata a ba su kulawa ta musamman; a ji ta bakinsu, a rarrashe su domin su daina yin abin da suke yi".

Tsohon shugaban na Najeriya na magana ne a daidai lokacin da wata kungiya mai suna The Global Commission on Drug Policy - wacce fitattun shugabannin duniya ke cikinta, ta yi kira a sake yin nazari kan yadda ake magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi.

Kungiyar, wacce ta fitar da sabon rahoto kan yadda ake tunkarar yaki da miyagun kwayoyi, ta ce tsangwamar da ake yi wa masu shaye-shayen kwayoyin tana yin kafar-ungulu a yakin da ake yi da kwayoyin.

Cif Olusegun Obasanjo shi ne shugaban kungiyar reshen Afirka ta Yamma.

Labarai masu alaka