Buhari na sakaci kan tattalin arziki —Obasanjo

Buhari ya mayar da hankali kan yakin da ta'addanci, in ji Obasanjo Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Buhari ya mayar da hankali kan yakin da ta'addanci, in ji Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce Shugaba Muhammadu Buhari yana sakaci sosai a bangaren tattalin arziki duk da koke-koken da 'yan kasar ke yi.

Cif Obasanjo ya bayyana haka ne a wata hira ta musamman da BBC.

A cewarsa, "Akwai bukatar ya kai ga mataki na gaba [a yaki da kungiyar Boko Haram], amma ba tare da an yi watsi da bangaren tattalin arziki ba, domin tattalin arzikin kasa na cikin mummunan yanayi, kowane dan Nijeriya na kokawa"

"Ba za ka ce don kana yaki da Boko Haram shi ke nan ba za ka kula da wannan bangare na rayuwar illahin jama'ar kasa ba. Dole mu san cewa galibi, matsalar ta tayar da kayar baya ta taso ne saboda an yi watsi da wannan yanki ta fuskar ci gaba".

Tsohon shugaban na Najeriya ya bayyana damuwa kan yiwuwar shigowar kungiyar ISIS Najeriya sakamakon komawar 'yan kasar gida daga Libya.

Ya ce, "Baya ga mutanen da ake mayar wa Najeriya, ina kuma da damuwa game da cewa bayan da ake tarwatsa 'yan ISIS daga Iraqi da Syria, wuri daya tilo da za su iya komawa yanzu ita ce Libya inda ake da dukkan yanayin da kungiya kamar ISIS za ta rayu.

"Kasa ce da kusan ba ta da gwamnati, amma kuma take da dimbin albarkatun kasa na fetur da iskar gas. ISIS za ta so ta yi amfani da wannan, kuma idan suka samu damar rike wannan arziki, to za su samu damar yada miyagun ayyukansu a illahirin yankin Sahel; Kuma kasa kamar Nijerya, kai ba Nijeriya kadai, dukkan kasashe da ke arewacin Kogin Congo, za su kasance cikin hadari", in ji Obasanjo.

Labarai masu alaka