Ana shari'ar dan sandan da ya kashe mutum 59

map

An fara shari'ar wani tsohon dan sanda na Rasha wanda dama an yanke masa hukunci domin kashe wasu mata 22 a birnin Irkutsk na Siberia domin tuhumarsa da ake cewa ya kashe wasu gomman mutane.

Mikhail Popkov mai shekara 53 da haihuwa ya gaya wa jami'ai da kansa cewa ya kashe wasu karin mutum 59 a shekarun 1992 zuwa 2010.

Idan aka tabbatar da laifukan nasa, zai zama mutumin da kashe mutane mafi yawa a jere a tarihin Rasha.

Kafafen labarai na Rasha sun lakaba masa sunan "Mahaukacin Angarsk".

A hali yanzu Popkov na zaman dauri ne a kurkuku har na tsawon ransa bayan da aka yanke masa hukunci a 2015 saboda yi wa mata 22 fyade da kuma kashe su,

Ya kuma yi yunkurin kashe wasu matan guda biyu.

Yawancin wadanda Popokov ya kashe mata ne masu shekaru daga 16 zuwa 40, amma ya kashe namiji daya wanda dan sanda ne kamarsa.

Masu shigar da kara sun ce Popkov ya kashe matan ne bayan ya dauke su a motarsa bayan ya yaudaresu da cewa zai taimake su ne ya sauke su a wurin da zasu.

Idan aka same shi da laifin kisan dukkan mutane 81, zai kasance ya gota yawan wadanda wani mutum mai suna Alexander Pichushkin, wanda ya kashe mutum 48 da kuma Andrei Chikatilo da shi kuma ya kashe mutum 52 a zamanin tsohuwar tarayyar Sobiyet.

Image caption Hoton Andrei Chikatilo wanda ya kashe mutum 52 a zamanin tsohuwar tarayyar Sobiyet hukunci

Labarai masu alaka