Sojin Myanmar sun yarda sun kashe 'yan Rohingya

Fire engulfs a village in Rakhine on 7 September 2017 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kone kauyuka masu yawa a lokaciin wannan rikicin da ya barke a watan Agustar bar.

A karon farko, sojin Myanmar sun yarda cewa lallai sun kashe 'yan kabilar Rohingya a jihar Rakhine.

Rundunar ta ce wani bincike da ta gudanar ya tabbatar da cewa wasu sojojin kasar suna da hannu wajen kisan mutum 10 a kauyen Inn Din dake kusa da Maungdaw.

Rahoton ya kuma ce sojojin su hudu sun taimaka wa mutanen kauyen kai wa wadanda suka kira "'yan ta'addan Bengali" harin ramuwar gayya.

An sha tuhumar gwamntin Myanmar da yunkurin share 'yan kabilar Rohingya daga doron kasa a jihar Rakhine.

Fiye da 'yan Rohingya 650,000 sun tsere zuwa makwabciyar kasar Bangladesh tun bayan wannan tashin hankalin da ya barke a watan Agusta.

An sami rahotannin cewa sojin Myanmar sun kashe dubban mutane kuma sun yi wa mata fyade.

'Yan Rohingyan sun tuhumi sojin kasar da mara wa 'yan banga mabiya addinin Bhudda da laifukan yaki

Amma rundunar sojin kasar ta sha musanta wannan zargin, inda take kafewa da cewa tana yakar 'yan tawayen Rohingya ne kawai.

Wannan amincewar da sojojin Myanmar suka yi ya bada mamaki.

A watan Nuwamba sojojin sun kakkabe hanunsu daga laifukan da aka tuhume su da aikatawa na kisan kare dangi akan 'yan Rohingya, da kona musu kauyukansu da yi wa mata da 'yan mata fyade har da satar kayansu.

Labarai masu alaka