Nigeria: An tura sojoji arewa ta tsakiya

Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rikicin makiyaya da manoma na daga manyan kalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta

Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta tura runduna ta musamman a wasu jihohin arewa guda uku inda rikici tsakanin makiyaya da manoma ya janyo hasarar rayukan mutane da dama.

An tura rundunar ne a jihohin Benue da Taraba da Nasarawa domin magance rikicin na makiyaya da manoma.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta bayyana cewa hedikwatar tsaron kasar ta tura dakaru na musamman a jihohin guda uku domin bayar da kariya ga al'ummomin yankin daga hare-hare.

Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani kan adadin dakarun ba, da kuma yanayin aikin da za su gudanar.

Matakin tura dakarun na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin jihar Benue ke binne mutane 80 wadanda aka kashe a wani rikici da ya barke a makon jiya.

Mutanen dai sun gamu da ajalinsu ne a rikicin da ya faru tsakanin makiyaya da manoma a kananan hukumomun Gomo da Logo.

Gwamnatin jihar Benue ta daura alhakin kisan a kan kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah, zargin da kungiyar ta musunta.

Sakataren kungiyar na kasa Usman Baba Ganjarma ya shaidiwa BBC cewa mutanensu ne ake muzgunawa.

Mutane sama da 100 ne dai suka mutu cikin mako daya a jihohin Benue da Taraba da Nasarawa.

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane 9, da ta ce mambobin wata kungiya ce da gwamatin jihar ta kafa domin tabbatar da zaman lafiya da aka fi sani da 'live stock guard'.

Sojojin sun bayyana cewa mutanen da aka kama da muggan makamai suna samun goyon bayan gwamnatin jihar ne, kuma yaran wani makusancin gwamnan ne mai kula da harkar makiyaya Alhaji Ali Tashako, wanda aka ruwaito yana ba su bindigogi da kuma kudin albashi duk wata.

Bayanan da sojojin suka fitar dai sun ce dakarun kungiyar sun haura 700.

Sai dai ko da yake Ali Tashako ya musanta cewa yaransa suna daukar muggan makamai, kuma yana ba su horo.

Image caption Gwamnatin Benue ta haramta yin kiwon sake a fadin kasar

Gwamnatin Najeriya dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan gaggauta daukar matakan kawo karshen rikicin.

Tuni dai babban sufeton 'yan sanda ya tare a jihar ta Benue domin kawo karshen tashe-tashen hankulan bisa umarnin Shugaban kasa.

Kuma bayanai sun nuna cewa a yau Alhamis shugaban 'yan sandan ya jagoranci wani babban taro na tsaro a jihar Nasarawa tare da masu ruwa da tsaki kan yadda za a magance rikice-rikicen.

Rikicin makiyaya da manoma dai musamman a jihohin tsakiyar Nageriya na daga manyan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta, baya ga rikicin Boko Haram, da matsalar sacewa da garkuwa da mutane da rikice-rikicen kabilanci da na addini da suka addabi kasar.

Labarai masu alaka