Boka ya hana mata masu jinin al'ada tsallaka rafi

Boko ya haramta wa masu jinin al'ada tsallaka rafi Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Haramcin Bokan ya shafi dukkanin matan da ke yankin Kyekyewerein

Sarakunan gargajiya a Ghana sun haramta wa dalibai mata masu jinin al'ada tsallaka rafi a yayin zuwa makaranta.

Wani Boka da ake yi wa bauta ne ya bayar da umurnin hana wa 'yan matan ratso rafin na Ofin domin zuwa makaranta.

Sannan bokan ya haramta wa mata tsallaka rafin a duk ranar Talata.

Haramcin dai ya fusata 'yan rajin kare hakkin yara, inda dole sai 'yan matan sun tsallaka rafin domin isa makaranta a Kyekyewerein.

Hakan dai na nufin 'yan matan da ke yankin gabacin Denkyira a tsakiyar kasar ba za su je makaranta ba a lokacin da suke jinin al'ada.

Jekadiyar da ke kula da lafiyar mata a hukumar UNESCO Shamima Muslmin Alhassan ta shaidawa BBC cewa, haramcin ya saba 'yancin ilimi ga 'ya'ya mata.

"Ga alama dai Bokaye na da karfi iko, ya kamata wani lokaci a tsure su kan ayyukan da suke musamman yadda suke haramta wa mutane gudanar da wasu ayyuka, domin su fadi yadda suke amfani da karfin ikon da ake ba su." A cewarta.

Rafin Ofin dai shi ne ya yi iyaka tsakanin Ashanti da yankin tsakiya.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da kimiya da ilimi da al'adu ta UNESCO ta ce mace daya cikin 10 a yankin na kauracewa makaranta a lokacin da suke jinin al'ada.

Ministan yankin tsakiya Kwamena Duncan ya nuna alamun zai zauna tare da ministan yankin Ashanti domin samar da mafita kan lamarin.

Wasu Al'adun kasashe dai na nuna kyama ga mata masu jinin al'ada.

Labarai masu alaka