An sallami Yusuf Buhari daga asibiti a Abuja

Buhari Hakkin mallakar hoto Facebook/Presidency
Image caption Yusuf Buhari ya yi hadarin ne a ranar Kirsimeti a Abuja

An sallami dan Shugaban kasar Najeriya Yusuf Buhari daga asibiti bayan hadarin da ya yi a watan jiya, kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana.

Maitaimaka wa shugaban kasar kan harkar yada labarai Bashir Ahmed ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

An sallame shi ne daga asibiti, inda ya yi jinyar munanan raunukkan da ya ji lokacin wani hadarin babur a birnin Abuja.

Sai dai da BBC ta tuntube shi don neman karin haske, Bashir Ahmed ya tabbatar da sallamarsa amma kuma daga nan bai yi karin haske ba game da halin da yake ciki yayin sallamar tasa.

Da yammacin ranar Kirstimetin aka kwantar da shi a asibitin sakamakon karaya da kuma raunin da ya ji a kansa sakamakon hadarin.

A cewar wata sanarwa daga fadar shugaban kasar wadda mai ba shugaban shawara na musamman kan watsa labarai Femi Adesina ya fitar ranar Juma'a.

Wadannan bayanin na kunshe a cikin wata wasika wadda asibitin Ceder Crest da ke nan Abuja inda Yusuf din ke jinya ta aikowa fadar shugaban.

A cikin wasikar mai dauke da sa hannun shugaban asibitin Dokta Felix Ogedegbe, asibitin ya bayyana cewa a cikin mako daya bayan shigar da Yusuf a sashen wadanda ke cikin mawuyacin da kuma yi masa aikin tiyata na gaggawa "jikin nasa ya yi sauki."

"Kuma tun daga wannan makon na farkon lafiyarsa ke inganta kuma yanzu ya ji saukin da a iya sallamarsa kowane lokaci."

Hakazalika asibitin ya ce dan shugaban ne kawai ya samu raunuka domin ba wani tare da shi a lokacin hadarin sabanin wasu rahotannin da ke cewa ya samu hadarin tare da wani abokinsa.

Bugu da kari ya musanta cewa an kwantar da mahaifiyar yaron, Aisha Buhari, a asibitin saboda halin kaduwa da shiga sakamakon halin dan nata ya shiga.

Duka fadar shugaban da kuma asibitin ba su fadi takamaimai lokacin da za a salami dan shugaban daga asibitin ba kuma ba su nuna wasu hotunnan da kara tabbatar da gaskiyar wannan bayanin ba.

A zahiri dai asibitin na mayar da martani ne ga wani labarai da jaridar nan ta 'yan Najeriya mazauna Amurka ta Sahara Reporters ta wallafa a shekaran jiya Laraba.

Kafar yada labaran ta ce za a fita da dan shugaban kasan zuwa kasar Jamus domin ci gaba da yi masa magani saboda jikinsa baya karbar magani yadda ake bukata a asibitin na Cedar Crest.

Ta ce an kasa fita da shi tun lokacin hadarin ya afku ne saboda munin raunukkan da ya samu a kwakwalwarsa.

Da yammacin ranar Litinin 25 ga watan Disamba ne dai Yusuf Buhari ya fadi da babur a unguwar Gwarimpa da ke nan birnin Abuja inda ya samu karaya a kafarsa da kuma wani mummunan rauni ga kansa.

Labarai masu alaka