'Yan Shi'a sun bukaci a saki El-Zakzaky

A watan Disambar 2015 aka kama El-Zakzaky Hakkin mallakar hoto Pr NIGERIA
Image caption A watan Disambar 2015 aka kama El-Zakzaky

Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka fi sani da 'yan Shi'a a Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar ta bi umarnin kotu ta saki Shugabanta Sheikh Ibrahim El-Zakzaky bayan ya yi magana da manema labarai karon farko tun bayan da kama shi.

Kakakin kungiyar Ibrahim Musa ya shaida wa BBC cewa bai kamata gwamnati ta ci gaba da tsare Malamin ba idan da gaske tana bin dokokin kasa.

A cewarsa, Malamin yana matukar bukatar a duba lafiyarsa sosai saboda rashin lafiya da tsufa.

Sai dai kwanakin baya ministan shari'ar kasar Abubakar Malami ya shaida wa BBC cewa suna ci gaba da tsare shi ne saboda sun daukaka kara a kan umarnin da kotunan suka bayar.

Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ce ya yi fama da karamin shanyewar jiki a cikin makon jiya.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a karon farko ranar Asabar tun bayan da aka kama shi fiye da shekara biyu da suka wuce.

Malamin addinin ya bayyana ne a Abuja tare da maidakinsa Zeenah wadda ake tsare da su tare.

Rundunar sojin kasa ta Najeriya ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan Disambar shekarar 2015 a Zaria da ke jihar Kaduna, bayan sojoji sun yi wa gidansa kawanya.

Wata sanarwa da kafar watsa labarai ta PR Nigeria fitar na dauke da hotunan Malamin a lokacin da yake jawabi ga 'yan jaridar.

Gidan talbijin na Channels ya ambato Sheikh El-Zakzaky na cewa yana nan a raye kuma lafiyarsa lau.

Ya kuma gode wa 'yan Najeriya saboda addu'o'in da suke yi masa.

A makon nan ne dai aka yi jitar-jitar cewa malamin ya rasu.

Ga yadda ganawarsa ta kasance da 'yan jarida:

'Yan jarida: Barka da rana?

'Yan jarida: Ko za ka iya ganawa da mu?

Sheikh El-Zakzaky: Idan sun amince kuma sun ba ni izini (kamar yadda ya ce cikin raha)

'Yan jarida: Wane hali kake ciki?

'Sheikh Zakzaky: Na samu shanyewar barin jiki a ranar Juma'a 5 ga watan Janairun bana

Sheikh Zakzaky: Jikin ya yi tsanani ranar Litinin, amma daga baya jikin ya yi sauki

'Yan jarida: Yaya kake ji yanzu haka?

Sheik El-Zakzaky: Ina samun sauki jami'an tsaro sun bari na gana da likitan. Ina godiya ga Allah. Ina samun sauki.

'Yan jarida: Kana da wani abu da za ka kara cewa.

Sheikh El-Zakzaky: Ina godiya ga addu'o'inku.

'Yan jarida: Mun gode

Sheikh El-Zakzaky: Na gode.

Hakkin mallakar hoto Pr NIGERIA
Image caption El-Zakzaky