Villarreal ta doke Madrid har gida

Ronaldo Hakkin mallakar hoto Getty Images

Kungiyar Villarreal ta doke Real Madrid a Bernabeu a wasan da suka fafata ranar Asabar a gasar La Liga.

Pablo Fornals ne ya jefa kwallo a ragar Madrid yayin da ya rage minti uku a tashi wasan.

Wannan rashin nasarar yana zuwa ne a daidai lokacin da kocin kungiyar Zinedine Zidane ya ke ci gaba da fuskantar matsin lamba.

Yanzu Madrid tana mataki na hudu ne a teburin gasar, abin da ya sa wadansu suke ganin kungiyar ba ta da tabbacin samun gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai.

Ga sakamakon wasannin da aka buga a Gasar Premier Ingila ranar Asabar

  • Chelsea 0-0 Leicester
  • Crystal Palace 1-0 Burnley
  • Huddersfield 1-4 West Ham
  • Newcastle 1-1 Swansea
  • Watford 2-2 Southampton
  • West Brom 2-0 Brighton
  • Tottenham 4-0 Everton

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka