Ba na goyon bayan Fulanin da ake zargi da kashe mutane — Buhari

Shugaba Buhari ya bukaci masu amfani da shafukan zumunta su yi hattara da makaryata Hakkin mallakar hoto TWITTER
Image caption Shugaba Buhari ya bukaci masu amfani da shafukan zumunta su yi hattara da makaryata

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba shi ne ya wallafa sakon da ke goyon bayan Fulani makiyayan da ake zargi da kisan mutane a jihar Benue da ke tsakiyar kasar ba.

Wani sako da ya wallafa a shafinsa na intanet, Shugaba Buhari ya yi tur da masu kashe-kashen jama'a a dukkan fadin kasar.

Yana mayar da martani ne kan wani sako da aka yi zargin shi ya wallafa a shafinsa na Twitter, wanda ke cewa "Fulani na kare kansu ne daga barayi, don haka ya kamata a bar jami'an tsaro su yi bincike kan lamarin."

Shugaban ya ce ba shi ya wallafa sakon ba kuma ya yi Alla-wadai da kashe-kashen.

"An wallafa wani sakon Twitter da ke yawo cikin jama'a da aka ce daga shafina @MBuhari ne. Wannan mugun sakon yana so ya halasta kisan da makiyaya ke yi, inda ya ce suna kare kansu ne.

"Ina mai nisanta kaina daga wannan sakon. Shugaba Buhari na kan bakansa na yin tur da kisan da aka yi a Benue da sauran wurare.", in ji sakon.

Ya kara da cewa Shugaba Buhari na nan kan matsayinsa na umarnin da ya bayar kan a hukunta masu kashe-kashen mutanea dukkan fadin kasar.

A cewar shugaban, tuni aka soma kama mutanen da ake zargi da yin kashe-kashe a jihar ta Benue.

Shugaba Buhari na yin wannan bayani ne a daidai lokacin da al'umar Hausawa da Fulani da ke jihar Benue suka yi zargin cewa 'yan kabilar Tibi sun far musu a karshen mako, inda suka kashe wasu mutane.

Sai dai wasu Tibi sun shaida wa BBC cewa zargin ba shi da tushe ballantana makama.

Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Shugaba Buhari ya gana da gwamnan Benue kan lamarin

Labarai masu alaka