Buhari ya jefa Nigeria a halin koma-baya —Fasto Bakare

Fasto Tunde Bakare Hakkin mallakar hoto TWITTER/TUNDE BAKARE

Mutumin da ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a shekarar 2011, Fasto Tunde Bakare, ya ce gwamnatin shugaban kasar ta jefa Najeriya a halin ci baya maimakon ci gaba.

Mr Bakare ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da huduba a Cocinsa da ke birnin Lagos na kudu maso yammacin kasar.

A cewarsa, "Wannan gwamnatin ta kafu ne a jigo uku, wadanda suka hada da magance matsalar tsaro da samar da ayyuka da yaki da cin hanci, amma idan ka duba babu abin da za ka gani sai alamomin ci gaba.

"Tsakanin shekarar 2015 da 2017, adadin matasa marasa aiki ya tashi daga mutum miliyan shida zuwa miliyan 16."

Malamin addinin Kiristan ya kara da cewa a bangaren yaki da cin hanci, wanda ake ganin ke da muhimmanci, gwamnati ta gaza.

"Misali, a watan Afrilun 2017, Gwamnatin Tarayya ta sha kaye a shari'u hudu manya cikin sa'o'i 96. Ta sha kaye ne a yayin da ta gaza tabbatar da mukamin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC," in ji Tunde Bakare.

Ya kara da cewa babu abin da ya dada tabbatar da gazawar gwamnatin Shugaba buhari kamar rashin iya magance matsalar tsaro.

Ya ce, "Muna jinjina mata kan yaki da Boko Haram, duk da koma bayan da aka samu a yakin a kwanakin baya bayan nan. Amma abin da yake matukar tayar da hankali shi ne yadda Fulani makiyaya ke ci gaba da kai hare-hare babu kakkautawa kan kauyuka a jihohi da dama."

Fasto Bakare ya ce da alama da gangan gwamnatin ta bari ake ci gaba da kashe-kashe "saboda ba ta dauki wasu matakan rigakafi faruwar kashe-kashen ba duk da gargadin da aka rika yi.

"Kazalika duk da faruwar irin wadannan kashe-kashe, ciki har da wadanda aka yi a jihar Adamawa kwanakin baya, Shugaban kasa, a jawabinsa na sabuwar shekara, bai ce komai a kan batun ba."

Ya zuwa yanzu dai, gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani kan wadannan zarge-zarge ba.

Labarai masu alaka