An kori shugabar Liberia Ellen Johnson Sirleaf daga jam'iyyarta

Ellen Johnson Sirleaf speaks on stage in New York (September 2017) Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ellen Johnson Sirleaf ta zama shugabar Liberia a 2006

An kori shugabar Liberia mai barin gado daga jam'iyyarta, saboda zargin kin goyon bayan mataimakinta a zabe domin ya gaje ta.

An zargi Ellen Johnson Sirleaf da laifin zuga 'yan kasar su ki zaben mataimakinta, Joseph Boakai.

Tsohon fitaccen dan kwallon kafa George Weah ne ya lashe zaben da aka yi a watan Disamba, inda ya doke Mr Boakai.

Ms Sirleaf, wacce ta ci kyautar Nobel ta Zaman Lafiya, ita ce mace ta farko da ta zama shugabar kasa a Afirka.

Kakakin jam'iyya mai mulki Unity Party ya ce Ms Sirleaf ta keta kundin tsarin mulkinsu domin kuwa an gan ta tana yi wa Mr Weah, wanda ya tsaya takara a jam'iyyar the Coalition for Democratic Change, yakin neman zabe.

Ms Sirleaf ba ta ce komai ba har yanzu game da korar tata.

Nan gaba a wannan watan ne za a rantsar da Mr Weah.

Wannan ne karon farko da za a samu sauyin gwamnati a kasar tun daga shekarar 1944.

Ms Sirleaf ta samu goyon baya a ciki da wajen Liberia saboda aikin da ta yi na dawo da zaman lafiya bayan yakin basasa.

Labarai masu alaka