Mu ba mu yarda a dawo da Rahama Sadau ba – Kabiru Maikaba

Kabiru Maikaba Hakkin mallakar hoto Facebook/Kabiru Maikaba
Image caption Kabiru Maikaba ya ce MOPPAN ba za ta yafe wa Rahama Sadau ba sai ta zo an zauna da ita

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar Masu Shirya Fina-Finan Hausa (MOPPAN), Alhaji Kabiru Mai Kaba ya ce ba su yarda da matakin gafartawa Rahama Sadau wanda hukumar tace fina-finan jihar Kano ta yi a makon jiya.

Mai Kaba ya mayar da martani ne ga shugaban hukumar tace fina-finai Isma'ila Na'abba Afakalla.

A ranar Talata ne Afakalla, ya shaida wa BBC cewa, a shirye suke su fara tace fina-finan da jarumar za ta rika fitowa a cikinsu da kuma wadanda take daukar nauyinsu.

A watan Oktoban da ya gabata ne shahararriyar jarumar ta fito fili ta nemi gafarar duk wani mutum da bai ji dadi ba sakamakon fitowar da ta yi a wani bidiyon waka tana "rungumar" wani mawaki.

  • Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da muka yi da Kabiru Mai Kaba
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
'Afakallahu na yi wa MOPPAN katsalandan'

Labarai masu alaka