CHAN 2018: Nigeria za ta kara da Rwanda

nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta 'yan wasan da ke murza-leda a Afirka za ta kara da ta Rwanda a ranar Litinin.

Kasashen biyu za su fafata ne a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Morocco ke karbar bakuncin wasannin shekarar nan.

A dai ranar ta Litinin Libya za ta kece raini da Equatorial Guinea wadanda suke rukuni na uku tare da Najeriya da Rwanda.

Wasanni hudu aka tsara buga wa a ranar Lahadi da suka hada da Morocco da Mauritania a fafatawar rukunin farko.

Sauran wasan rukunin farko shi ne tsakanin Guinea da Sudan.

Haka a ranar ta Lahadi rukuni na biyu zai yi wasan farko tsakanin Ivory Coast da Namibia da kece-raini tsakanin Zambia da Uganda.

Karanta wadansu karin labarai

Labarai masu alaka