Ba na nuna wariyar launin fata – Trump

Donald Trump speaks to reporters at Trump gold club. Hakkin mallakar hoto AFP/Getty

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce shi ba mutum ba ne mai nuna wariyar launin fata bayan an zarge shi da siffanta kasashen Afirka da wulakantattu.

Rahotanni sun ce shugaban ya yi amfani da kalmar ne a makon jiya yayin da yake wani taro kan batun shige da fice a fadarsa.

Shugaban ya bayyana wa mane labarai cewa: "Ni ba mai nuna wariya ba ne. Ni ne mutumin da na fi duk wani mutum da kuka taba ganawa da shi karancin nuna wariyar launin fata"

Wannan ne karon farko da shugaban yake mayar da martani kai-tsaye game da zarginsa da yin kalaman.

Trump ya musanta hakan yayin da yake wata ganawa da manema labarai a ranar Lahadi.

A makon jiya ne wadansu rahotanni suka ambato shugaban Amurka Donald Trump yana yin maganganun wulakanci kan 'yan ci-ranin da suka fito daga kasashen Haiti, El Salvador da Afirka.

Labarai masu alaka