'Neman ruwa mai tsafta ne ke hana ni zuwa makaranta'

The foothills of the Gurue mountains Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau

Mario Macilau yana da shekara 23 a 2007, a lokacin da ya bude wayar mahaifiyarsa zai dauki hoto. Daukar hoto ba sabon abu ba ne a wurinsa, saboda ya saba da daukar hotunan abin da yake faruwa a garinsu da ke Maputo, babban birnin Mozambique, tun yana dan shekara 14.

Ya saba daukar hotunan yaran da suke gararanba a titi, inda suke gwamutsuwa a kangon gine-ginen da aka yi a Maputo, da na ma'aikatan kamfanin siminti na kasar. Yanzu ya karkata akalarsa kan batun ruwan sha.

Ya dauki wadannan hotunan ne a karshen shekarar 2017, tare da hadin gwiwar kungiyar da ke rajin samar da tsaftataccen ruwa ta "WaterAid for Untapped" wadanda za su ci gaba da yi har zuwa karshen watan Janairu. Har zuwa sama da shekara uku masu zuwa Macilau zai ci gaba da adana tarihin sauye-sauyen da shirin samar da ingantaccen ruwan sha da bandakuna ga al'ummar da suke Gundumar Coamba a Mozambique.

Wasu yara uku suna murmushi Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau
Kamr wani tsohon manomi Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau
Josefina ta dauko ruwa a bokiti zata kai gida daga Rio Naranja. Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau

Shekarun Josefina da Eudicia 12, kuma ba sa samun damar zuwa makaranta sau hudu a mako saboda fafutukar nemo ruwa.

Suna tafiya Rio Naranja, wata korama da take samun ruwa daga kogin Muassi, wanda yake shi ne babbar hanyar da mazauna kauyen Muassi suke samun ruwa.

Koramar ma ba ta kwaranya, kuma launin ruwan da 'yan matan ke debowa ya sauya zuwa madara, in ji Macilau.

A cewar WaterAid, a fadin duniya kusan daya daga cikin yara tara ba sa samun tsaftataccen ruwan sha a kusa da muhallansu, kuma daya daga cikin uku ba su da bandaki mai kyau.

Kowace rana, akalla yara 800 'yan kasa da shekaru biyar ne ke mutuwa sakamakon amai da gudawa, wadanda gurbataccen ruwan sha da rashin tsafta ke haddasawa.

The Rio Nanjana with its stagnant water Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau
Josefina and Eudicia climb a hill with buckets balanced on their heads. Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau
A bucket in the river Lurio after the rains. Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau

Lokacin damina, ba a amfani da kogin Lurio wajen samar da ruwan sha saboda yana kusa da bola da bayan-gidan da idan an yi ruwan sama sukan kwaranya cikinsa.

A kauyen M'mele, gidajen da aka gina da tubalan kasa sun rushe sakamakon ambaliyar ruwa da mamakon ruwan sama a shekara uku da suka gabata.

Kuma shugaban kauyen ya ce mutane na kaurace wa yankin sakamakon matsalar ruwan sha.

A mud brick house destroyed by heavy rainfall and flooding Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau
An elderly farmer stands in his field, overlaid onto an image of a puddle of murky water Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau
Image caption Wani tsohon manomi a tsaye a gonarsa
Angelina with her daughter Irene in Sosina Masel Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau
Image caption Angelina da 'yarta Irene a Sosina Masel
Elisa Piassone and Zaida walk along the road between M'mele and Kimar Hakkin mallakar hoto WaterAid/ Mario Macilau
Image caption Elisa Piassone da Zaida na tafiya a kan hanyar da ke tsakanin M'mele da Kimar inda suke kokarin kai garin masara.

Hotunan na WaterAid da Mario Macilau ne

Labarai masu alaka