Boko Haram ta fitar da bidiyon 'yan matan Chibok

Shekau Hakkin mallakar hoto Twitter

Kungiyar Boko Haram a Najeriya ta fitar da wani sabon bidiyon da ke dauke da wasu daga cikin ragowar 'yan matan Chibok da kungiyar ta sace.Bidiyon ya nuna daya daga cikin matan sanye da shudin hijabi da farin nikabi tana mai fuskantar kemera, kewaye da wasu matan su kusan goma.

Daya daga cikinsu, wacce ta yi jawabi a cikin bidiyon, ta ce ba za su koma wurin iyayensu ba.

Ta yi kira ga iyayen su tuba.Kungiyar ta kuma fitar da wani bidiyon da ya nuna abin da masu tayar da kayar bayan suka kira jirgin yakin da suka kakkabo.Boko Haram tana kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya ne tun shekarar 2009, kuma ta kai hare-hare kasashe masu makwabtaka.

Yakin na Boko Haram dai ya yi sanadin mutuwar dubban mutane yayin da ya raba miliyoyi da gidajensu.Mayakan sun saci 'yan mata 276 daga makarantar sakandaren garin Chibok a shekarar 2014, lamarin da ya janyo Allah-wadai daga fadin duniya. Ana tunanin cewa mayakan suna rike da akalla 'yan matan na Chibok 100, bayan sun sake sauran 'yan matan.

Labarai masu alaka