An saki 'yan Boko Haram 244 da suka tuba

Abubakarr Shekau Hakkin mallakar hoto Reuters

Rundunar sojin Najeriya ta mika wa gwamnatin Borno 'yan Boko Haram kimanin 244 da suka tuba.

Rundunar sojin ta ce sai da suka bi matakai na sauya tunaninsu kafin ta sake su, kuma yanzu suna da damar yin cudanya da jama'a.

Babban kwamandan rundunar Lafiya dole da ke yaki da Boko Haram ne ya mika mutanen ga gwamnan Borno, daya daga cikin jihohin yankin arewa maso gabashi da suka shafe shekaru 8 suna fama da rikicin Boko Haram.

'Yan boko Haram din da aka saka sun hada da mata da yara kanana. Sai dai masana tsaro na bayyana fargaba kan ko mayakan da aka saka sun tuba ne har abada.

Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a farkon watan Janairu, ta ce kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 700 suka mika wuya a yankin Munguno bayan luguden wuta da ta yi a sansanonin da suke boye.

Da dadewa ne dai gwamnatin Najeriya ta bude kofar tuba ga 'yan Boko Haram, ta hanyar wani shirin "Operation safe Corridor", inda za a sauya musu mugun tunanin da yake zukatansu da kuma ba su ayyukan yi.

A watan Oktoban da ya gabata ne Najeriya ta fara shari'ar mutane sama da 6,000 da ake zargi 'yan Boko Haram ne, wadanda aka shafe shekaru ana tsare da su ba tare da gabatar da su a kotu ba.

Sakin 'yan Boko Haram din dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya fitar da sabon faifan bidiyo da ke nuna sauran 'yan matan sakandaren garin Chibok da aka yi awon gaba da su tun a 2014 wadanda kuma suke ci gaba da garkuwa da su.

Labarai masu alaka