Boko Haram ta kai hari Adamawa

Yankin Madagali dai a jihar adamawa ya sha fuskantar hare-haren Boko Haram. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yankin Madagali dai a jihar adamawa ya sha fuskantar hare-haren Boko Haram.

Boko Haram ta kai sabon hari Pallam da ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum uku da jikkkata wasu.

Pallam dai shi ne mahaifar mataimakin shugaban majalisar jihar Adamawa, Emmanuel Tsamdu.

Kwamishinan yada labarai na Jihar ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce mutum uku ne suka mutu.

Ya ce mayakan sun kwashi kayayyaki kafin su cinna wa gidaje wuta.

Wasu bayanai na cewa, mayakan sun shiga garin na Pallam ne da daddare misalin karfe 11, inda suka fara harbe-harbe da kuma kona gidaje.

Sannan rahotanni sun ce mayakan sun yi awon gaba da wasu mutane da ba a bayyana adadinsu ba.

Harin ya zo ne bayan mako daya da Boko Haram ta kaddamar da wani hari makamancin haka a yankin kusa da Wanu, da Kamale da mazauna yankin Kafin Hausa a Michika da kuma wasu yankunan Madagali.

Yankin Madagali dai a jihar adamawa ya sha fuskantar hare-haren Boko Haram.

Harin na zuwa ne a yayin da rundunar sojin Najeriya ta ce ta mika wa gwamnatin Borno 'yan Boko Haram kimanin 244 da suka tuba.

Kuma wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya fitar da sabon faifan bidiyo da ke nuna sauran 'yan matan sakandaren garin Chibok da aka yi awon gaba da su tun a 2014 wadanda kuma suke ci gaba da garkuwa da su.

Labarai masu alaka