An sace shanu fiye da 300 a jihar Plateau

Shanu Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wadansu barayin shanu sun sace shanun makiyaya fiye da guda 300 da kuma awaki da dama a jihar Filato, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jami'in kungiyar Fulani makiyaya ta MIYETTI Allah Malam Muhammad Abdullahi ya ce "an sace dabbobin ne a yankin karamar hukumar Riyom amma mun yi imanin barayin sun fito da karamar hukumar Bassa mai makwabtaka."

Ya ce barayin sun "farma yaransu makiyaya a wani kauye da ake kira Gidan Ado, suka fatattake su suka kora su."

Daga nan ne sai yaran suka gudu suka tsere suka bar dabbobinsu, kamar yadda ya ce.

Har ila yau ya ce maharan sun tafi da wadansu dabbobin kimanin 150.

Ya ce abin bai tsaya a nan ba don daga bisani sun sake dawowa wani kauye a yankin, inda "suka kara sace shanu kimanin 200."

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Filato ASP Tyopev Mathias Terna ya tabbatar mana da sace shanun.

Sai dai ya ce jami'an tsaro da suka hada da sojoji da 'yan sanda "sun dukufa don ganin sun karbo shanun da kuma cafke barayin."

Kodayake jami'in kungiyar Fulanin ya ce jami'an tsaro sun shaida musu cewa sun ga "gawawwakin wadansu daga cikin shanun farko da aka sace kimanin guda 56."

Hakazalika ya ce an samu wadansu "fiye da guda 20 da aka yi musu munanan raunuka da ba za su iya tafiya ba." Kuma ya ce sauran shanun ba a gansu ba.

Amma ya ce akwai ragowa da aka kwato a hannun barayin wadanda suke hannun jami'an tsaro a halin yanzu.

Jami'in kungiyar MIYETTI Allah ya ce babu wanda ya rasa ransa ko kuma jikkata sanadiyyar wannan al'amarin.

A baya dai jihar ta yi fama da rikice-rikice tsakanin makiyaya da al'ummomin yankuna daban-daban galibinsu manoma.

Sai dai jihar ta samu kwanciyar hankali fiye da shekaru biyu da suka wuce.

Kodayake a baya-bayan nan matsalar rikice-rikicen ta yi kamari a jihohi makwabtanta kamarsu Benue da Taraba da kuma Adamawa.

Abin da ya sa gwamnatin kasar ta fitar da sanarwa kan cewa jami'anta sun kara shan damara don magance matsalar.

Labarai masu alaka