An sace shanu sama da 300 a Filato

Najeriya na fama da Rikicin makiyaya da manoma da matsalar satar shanu
Image caption Najeriya na fama da Rikicin makiyaya da manoma da matsalar satar shanu

Rahotanni daga jihar Filato na cewa wasu barayi sun sace shanu sama da 300 a karamar hukumar Riyom.

Makiyayan da aka sacewa shanun sun ce barayin sun fito ne daga karamar hukumar Bassa, sannan suka yi gaba da daruruwan shanun.

Wani shugaba a kungiyar fulani makiyaya ta Myatti Allah a jihar filato Malam Muhammad Nura Abdullahi ya shaidawa BBC cewa barayin sun farwa makiyaya a kauyen gidan Ado da ke karamar hukumar Riyom, inda suka fatattaki makiyayan sannan suka kora shanu kimanin 150.

"A tsakar dare sun sake dawowa kauyen Danwal a karamar hukumar ta Riyom suka sake daukar shanu kusan 200", Inji Malam Abdullahi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Filato ya tabbatar da satar shanun, sai dai ya ce sun dukufa wajen gano su tare da farautar barayin.

Wasu bayanai dai sun ce Shanu kimanin 50 daga wadanda aka sace duka an kashe su, sannan jami'an tsaron sun gano wasu da ransu.

A baya-bayan nan rikici tsakanin makiyaya da manoma ya janyo asarar rayuka a jihohin Taraba da Benue da kuma Adamawa.

Labarai masu alaka