Kalli bidiyo mai ban-mamaki na yadda aka jefo yaro daga benen da ke ci da wuta

Kalli bidiyo mai ban-mamaki na yadda aka jefo yaro daga benen da ke ci da wuta, kuma wani jami'in 'yan kwana-kwana ya cafke shi.

Bidiyon dai da ake yayatawa a shafukan sada zumunta ya nuna wani jami'in 'yan kwana-kwana a jihar Gorgia ta Amurka ya cafke wani yaron da aka jefo masa daga saman benen da ke ci da wuta. Gobarar dai ta raunata akalla mutum 12, ciki har da wasu yara. Amma babu wanda ya ji mummunan rauni a gobarar.