An cafke 'mai maganin samun cikin na bogi'

Mata na karbar maganin samun juna biyu na bogi a Guinea
Image caption Mata na karbar maganin samun juna biyu na bogi a Guinea

'Yan sanda a Guinea sun kama wata mai maganin gargajiya bisa zarginta da ba wa mata fiye da 100 maganin da ta ce zai sa su samu juna biyu.

Matar mai suna N'na Fanta Camara ta karbi makudan kudade daga hannun matan da ke neman haihuwa da zimmar zata ba su maganin da zai taimaka su samu juna biyu.

Ms Camara ta kan ba wa matan hade-haden ganyayyaki da wasu itatuwa.

Yanzu haka dai an dai kama mai maganin gargajiyar tare da wasu abokan aikinta mutum biyu.

Kuma tuni matan da suka karbi maganin matar suka gudanar da zanga-zanga a wajen ofishin 'yan sandan da ake tsare da ita a Conakry babban birnin kasar.

Ms Camara dai ta musanta zargin aikata ba dai-dai ba.Wasu matan da suka yi amfani da maganin matar sun ce sun fuskanci yanayi na alamun mai ciki fiye da shekara guda, amma kuma da suka je asibiti aka gwada su sai aka ga ba bu alamun juna biyu a tare da su.

Labarai masu alaka