Wayar Salula ta taimaka an gano budurwar da aka sace

Wayar salula ta taimaka an gano matar da aka sace tsawon kwanaki uku Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wayar salula ta taimaka an gano matar da aka sace tsawon kwanaki uku

An gano wata budurwa 'yar shekara 19 da ta ce an sace ta a Belgium bayan da ta yi amfani da wayarta ta salula ta aikawa da dan uwanta adireshin inda ta ke.

Matashiyar wadda daliba ce, ta ce wasu maza biyar ne suka sace ta a kofar wani gidan rawa da daddare a Brussels inda suka kai ta wani gida da ke kusa da birnin Charleroi suka kulle ta tsawon kwanaki uku.

Tuni dai aka kama mutum biyu da ake zargi inda ake tuhumarsu da laifin garkuwa da kuma fyade.

Sai dai kuma mutanen da ake zargi sun musanta aikata ba dai-dai ba.

Rahotanni sun ce matashiyar ta yi kokari ta dauki wayar salularta domin gano inda ta ke ta hanyar amfani da manhajar taswira ta Google.

Daga nan sai ta turawa dan uwanta adireshin wajen wanda ke da nisan kilomita 50 daga Brussels.

Bayan dan uwanta ya samu adireshin sai ya sanar da mahukunta a nan ne kuma suka isa wajen da ake tsare da ita.

Jami'an tsaron da suka kai samame a wajen, sun ce sun ga maza biyu a gidan inda kuma aka kama su.

Ana dai ci gaba da neman sauran mutum ukun da ake zargi.

Labarai masu alaka