Ina yin fim saboda mijina wayayye ne - Saratu Daso

Ina yin fim saboda mijina wayayye ne - Saratu Daso

Jarumar fina-finan Hausa Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso ta ce mijinta ya barta ta ringa fitowa a fina-finan Hausa duk da tana da aure saboda mijinta wayayye ne kuma mai ilimi.

Gabanin ta fara fina-finan hausa shekaru 18 da suka wuce, Saratu Daso malamar makaranta ce. Kuma ta ce aure bai hana ta fim ba. Sannan ta fito a wasu fina-finan turanci.