Zakzaky: 'Yan Shi'a sun fara zaman dirshen a Abuja

magoya bayan Zakzaky
Image caption 'Yan Shi'a sun ce za su ci gaba da zanga-zanga a Abuja

Kungiyar 'yan uwa musulmi, da aka fi sani da 'yan Shi'a a Najeriya ta kaddamar da wata zanga-zanga ta zaman dirshe a Abuja domin kiran a saki jagoranta da kuma iyalin shi.

'Yan shi'ar sun yi gangamin ne na tsawon sa'a daya, kuma sun ce za su ci gaba da yi a kullum har sai gwamnati ta saki jagoransu.

Rundunar sojin Najeriya ce ta kama Sheikh El-Zakzaky a watan Disamban shekarar 2015 a Zaria da ke jihar Kaduna, bayan wata arangama tsakanin jami'anta da magoya bayansa.

Zakzaky ya fito bainar jama'a a karon farko ranar Asabar din da ta gabata tun bayan da aka kama shi fiye da shekara biyu.

Malamin addinin ya bayyana ne a Abuja tare da mai dakinsa Zeenah wadda ake tsare da su tare.

Yayin da yake ganawa da manema labarai El-Zakzaky ya ce ya yi fama da karamin shanyewar jiki.

Labarai masu alaka